Gwamnatin Najeriya ta bayyana Juma’a 7 da Litinin 10 ga watan Afrilu a ranakun Easter

0 65

Gwamnatin Najeriya ta bayyana ranakun Juma’a 7 ga watan Afrilu da kuma Litinin 10 ga wata a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan bikin Easter na wannan shakarar.

Ministan al’amuran cikin gida na ƙasar Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da babban Sakataren ma’aikatar Shuaib Belgore ya fitar ranar Laraba.

Sanarwar ta buƙaci kiristocin ƙasar da su yi koyi da halayen sadaukarwa, da haɗin kai, da yafiya, da mutunta juna, da soyayya da zaman lafiya da haƙuri na Yesu Almasihu.

Ministan ya kuma yi kira al’ummar Kiristocin ƙasar da su su yi amfani da lokutan bukukuwan na Easter domin yi wa ƙasar addu’o’in samun zaman lafiya da kawo ƙarshen matsalar tsaro da ƙasar ke fuskanta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: