Gwamnatin tarayya ta bai wa kamfanin gine-gine mai suna Buildwell kwangilar Naira biliyan 14 domin sake gina babban titin tekun Mariner, don karfafa layin dogo.
Ministan ayyuka, Sanata David Umahi, wanda ya bayyana hakan a Legas, ya ce, ababen more rayuwa dake jihar Legas gwamnatin tarayya da ‘yan Najeriya na jin dadin su.
Ya ce an bayar da kwangilar ne bayan amincewar Majalisar Zartarwa ta Tarayya, inda ya kara da cewa Shugaba Bola Tinubu ya bada kwangilar yadda ya kamata.
A cewarsa, kamfanin Buildwell ya fara aiki kuma ba za a sami banbancin farashin kwangilar da za a kammala cikin watanni 12 ba.
Ya ce Buildwell zai yi amfani da kayan aiki masu nagarta don inganta hanyar.