Yan Kwankwasiyya masu son zaman lafiya ne — Kwankwaso

0 152

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New NNPP a zaben 2023, Rabi’u Musa Kwankwaso ya baiyana cewa mabiyan ɗarikar Kwankwasiyya mutane ne masu son zaman lafiya.

Kwankwaso, wanda shi ne jagoran NNPP da Kwankwasiyya na ƙasa, ya baiyana hakan a jawabi ga dimbin jama’a a wajen bikin Sallah, wanda gidauniyar Kwankwasiyya Foundation ta shirya domin bikin Babbar Sallah a jiya Talata a gidansa da ke Miller Road a Kano.

Kwankwaso ya zargi wadanda ya bayyana a matsayin makiyan jihar da haddasa rikicin da ya dabaibaye masarautar Kano.

Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, ya ce makiyan jihar, wadanda a yanzu su ne tsiraru, sun dage sai sun ga faduwar jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar.

Kwankwaso ya tuna cewa a 2019 sun lashe zaben gwamna amma “makiyan jihar” sun kwace nasararsu ta amfani da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta, INEC da Kotu.

“Na tabbata kun tuna a 2019, mun ci zabe a jihar nan (Kano), amma makiyan jihar sun yi mana magudi hanyar INEC, ta hanyar Kotu, da sauransu, amma abin da ya faru yanzu ya zama tarihi.

“Haka kuma, a wannan karon, a zaɓen 2023, mun ci zabe, gagara-badau, kuma an yi kokari sosai da makiyan Jihar, wadanda ‘yan tsiraru ne a nan— sun yi bakin kokarinsu wajen ganin an kwace mulkin, amma da yardar Allah, cikin hikimarSa, ya sa a ka tabbatar da adalci;

“Yanzu da alama makiya sun sake kawo hari! Ku na ganin abin da ke faruwa kan batun Masarauta, amma muna godiya ga duk masu goyon bayan matsayin gwamnati, mu daya ne kuma za mu ci gaba da zama daya.” ”

Kwankwaso ya bayyana cewa duk da makircin da aka kulla masa da kungiyar Kwankwasiyya, magoya bayan ta sun ci gaba da zaman lafiya.

“Bari kuma in yi amfani da wannan dama domin tunatar da ku cewa ‘yan Kwankwasiyya a duk inda suke, su kasance masu zaman lafiya, muna ci gaba da zaman lafiya,” inji shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: