Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet kan ma’adinai da sauran albarkatun ƙasa

0 175

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da shafin intanet jiya Talata wanda zai bai wa masu zuba jari damar samun cikakkun bayanai game da ma’adinai da sauran albarkatun ƙasa.

Da yake ƙaddamar da shafin na intanet, Ministan Harkokin Ma’adinai na kasa Dele Alake ya ce sun ɗauki matakin ne domin rage wahalhalun da masu zuba jari daga ƙasashen waje suke sha wurin samun bayanai game da ma’adinan da ƙasar take da su.

Nijeriya ce kan gaba a albarkatun man fetur a Afirka, kuma tana da tarin arzikin sauran albarkatun ƙasa irin su zinare, tama da ƙarafa, kwal, farar ƙasa, da sauransu.

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sha alwashin bunƙasa fannin ma’adinan domin samun kuɗaɗen-shiga da rage dogaro da man fetur, tana mai cewa a halin da ake ciki wannan fanni ba ya samar da sama da kashi ɗaya na kuɗin-shigar ta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: