Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Kudi Naira Biliyan 1 Domin Dukkan Jami’oi

0 169

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kudi kimanin naira biliyan 320.3 a matsayin kudaden ayyukan ga jami’oin kasar nan.
Babban sakatare a asusun lura da ilimin manyan makaranta Sonny Echono ya bayyana haka jiya a Abuja, yayi taron hakumar na shekara tare da dukkan shugabannin sassan jami’oin da suka ci gajiyar shirin.
Yace an gudanar da taron ne domin ra’ayoyi kan yunkurin da hukumar ke yi, domin sake inganta ayyukansu.
A cewar sa a shekarar 2023 da muke ciki kowace jami’a ta samu kudi da ya kai kimanin naira biliyan 1.1 da suka hada da miliyan 956 a matsayin kudin shekara da kuma naira miliyan 200 kudaden ayyuka na shiyya.
Echono ya lura cewa wannan shine adadi mafi yawa da asusun na TETfund ya taba fitarwa tun bayan kafa shi.
Ya yaba da yadda yace jami’oin kasar nan sun samu bunkasa a karkashin gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Leave a Reply