Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na tallafawa Nakasassu dubu 50,000 ga masu karamin karfi

0 98

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudurinta na tallafawa Nakasassu dubu 50,000 ta cikin shirin rabon kudade ga masu karamin karfi, wanda cutar Corona ta shafa.

Shugaban Hukumar Kula da Nakasassu ta Kasa Mista James Lalu, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai, inda ya ce a yau ne za’a fara karbar bayanan mutanen.

A cewarsa, fiye da shekaru Nakasassu suna fuskantar kalubalai a kasar nan, inda ya kara da cewa basu tallafin na daga cikin kudurin gwamnatin tarayya na yin tafiya dasu kafada-da-kafada.

Haka kuma ya ce za’a zakulo mutanen ne daga kananan hukumomi 744 na kasar nan, inda mafiya aka sarin su zasu fito ne daga kyauyika.

Shugaban Hukumar ya bukaci jihohi su tallafawa hukumar wajen bayar da bayanan mutanen da za’a tallafawa.

Mista James Lalu, ya ce kudade zasu zama tamkar Jari ne da Nakasassun da suke son fara Kasuwanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: