Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin tura tsoffin sojoji da suka yi ritaya domin taimakawa wajen kare yankunan ƙasar nan da ba a cika samun ikon gwamnati ba, a wani yunkuri na ƙarfafa tsaron ƙasa da kuma bunƙasa harkokin tattalin arziki a wuraren da suka dade suna fama da rikice-rikicen ta’addanci.
Wannan ya biyo bayan ƙaddamar da wani kwamitin mutane 18 da Ministan Tsaro Janar Christopher Musa ya kafa, domin dawo da waɗannan yankuna cikin tsarin tsaro da ci gaba, tare da sake farfaɗo da aikin Rundunar Nigerian Legion ta tsoffin sojoji.
An ƙaddamar da kwamitin ne a hedikwatar Ma’aikatar Tsaro da ke Abuja, inda ministan ya bayyana cewa shigar da tsoffin sojoji cikin ayyukan tsaro da ci gaba zai ƙara wa ayyukan sojojin da ke gudana ƙarfi, musamman a wuraren da ikon gwamnati ke da rauni.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan mataki na nuni da sauya dabarar tsaro daga dogaro da hare-haren soja kaɗai zuwa tsarin da ke haɗa tsaro da warware matsalolin zamantakewa da tattalin arziki.
Ministan ya jaddada cewa shirin wani ɓangare ne na ƙudirin gwamnati na tabbatar da jin daɗin tsoffin sojoji bayan ritaya, tare da ba su damar ci gaba da taka rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al-umma.
Ana sa ran cewa idan aka aiwatar da shirin yadda ya kamata, zai taimaka wajen rage ayyukan ta’addanci a yankunan da ba a kula da su, ya sauƙaƙa wa dakarun da ke kan gaba, tare da ƙarfafa tsaron da ya dogara da al’umma.