Gwamnatin Tarayya ta ce tana ci gaba da kokarin bude kananan guraren samar da Gas a unguwanni da kauyuka domin magance tashin farashin Gas a Najeriya

0 56

Gwamnatin Tarayya ta ce tana ci gaba da kokarin bude kananan guraren samar da Gas a unguwanni da kauyuka da dama, domin magance tashin farashin Gas a kasar.

Shugaban shirin fadada samar da Gas, Dr Mohammed Ibrahim ne ya bayyana haka a taron shekara-shekara nab ana na kungiyar masu sayar da gas ta kasa, jiya a birnin Fatakwal na jihar Ribas.

Mohammed Ibrahim ya ce gwamnatin tarayya ta mayar da hankali sosai wajen ganin an samar da gas ga ‘yan Najeriya kuma a farashi mai sauki nan gaba kadan.

Mohammed Ibrahim ya ce Najeriya ba ta da hurumin fitar da gas zuwa kasashen waje a lokacin da kasar ta gaza magance karancinsa a cikin kasa da kuma sauya fasalin masana’antar.

A cewarsa, kasarnan na da wadataccen gas a gabar tafkin Dahomy da bakin ruwan Neja-Delta, da bakin ruwan Bida, da gabar kogin Gondola da kuma gabar tafkin Chadi, da sauransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: