Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan 580 domin sayo manyan motocin ga hukumar NDLEA

0 43

Majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da kudi naira miliyan 580 da dubu 500 domin sayo manyan motocin yaki da muggan kwayoyi ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA).

Ministan shari’ah kuma babba lauyan tarayya, Abubakar Malami, shine ya sanar da haka ga manema labaran fadar shugaban kasa a karshen zaman majalisar wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta yau a Abuja.

Ministan yace an yanke shawarar sayo manyan motocin domin karfafawa da tsare rayukan jami’an NDLEA wadanda ke aiki tukuru tare da samun manyan nasarori.

A wani batun kuma, gwamnatin tarayya ta nanata cewa, ta kammala dukkan shirye-shiryen fara sharewa da gyara yankin Ogoni a jihar Rivers wanda mai mai malala ya lalata.

Ko’odinetan aikin gyaran muhalli a karkashin ma’aikatar muhalli, Dr Ferdinand Giadom, shine ya sanar da haka a karshen wani taron karuwa juna sani.

Leave a Reply

%d bloggers like this: