Gwamnatin Tarayya ta cewa ba ta cikin mafi kyawun matsayin sarrafa matatun man kasar

0 118

Gwamnatin Tarayya ta cewa ba ta cikin mafi kyawun matsayin sarrafa matatun man kasar.

Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur, Timipre Sylva, shine ya bayyana hakan a jiya  Alhamis.

Ya yi bayanin cewa gwamnati ba ta yarda da ra’ayin sayar da matatun mai a halin da suke ciki saboda irin wannan matakin zai sa  suka daga ‘yan kasa.

Ya kara da cewa  ba za a zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da halin da cibiyoyin ke ciki ba saboda ta gaji matatun mai da suka lalace.

Duk da wannan, ya ce gwamnati ta yanke shawarar tabbatar wa da ‘yan Najeriya cewa za a iya gyara matatun sannan a mayar da su cikin yanayin aiki. Bayan an gyara matatun man, ministan yace za’a tabbatarwa yan kasa yadda za’a gudanar dasu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: