Gwamnatin tarayya ta sake kwato kudade sama da Naira miliyan 120,000 da sauran wasu kadorori a kasashen waje

0 83

Gwamnatin tarayya a yau ta sanar da kwato kudade sama da naira miliyan dubu 120 da sauran kudaden waje, karkashin dokar kwato kudaden sata ta bana.

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya sanar da haka a Abuja a jerin tarukan shelar nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na 8.

An kaddamar da jerin tarukan ne a watan Oktoba domin bayyana takardu da nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Wannan karon Ministan Muhalli, Mohammed Abdullahi ne yayi jawabi.

A jawabin bude taro, Lai Mohammed yace yaki da rashawa na gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari yana bisa turba kamar yadda ya kamata.

Ya tunatar da cewa Shugaban Kasa a watan Mayu ya sanya hannu akan kudirin dokar kwato kudaden sata da wasu kudirorin biyu da nufin inganta kundin yaki da satar kudade da samar da kudaden ta’addanci na kasarnan.

Leave a Reply

%d bloggers like this: