Yan Majilisar dattijai sun umarci Gwamnan CBN da gyara sabuwar dokar cire kudi

0 82

A rahoton da BBC ta wallafa sunce Majalisar dattijan Najeriya ta ce za ta yi wa shugabannin babban bankin ƙasar (CBN) tambayoyi a kan sabuwar dokar da aka ɓullo da ita ta ƙayyade kuɗaɗen da ake cirewa a kowane mako.

Dama dai majalisar ta nuna damuwa kan lamarin a zaman da ta yi ranar Laraba, inda ta ce zai yi illa ga masu ƙananan sana’o’i.

A wata tattaunawa da BBC, sanata Adamu Bukachuwa ya ce “lokacin da muka ji wannan magana hankalinmu ya tashi, masu cin kasuwa irin na ƙauyuka yaushe dubu ɗari zai ishe su a mako.”

Sai dai ƴan majalisar sun ce lamarin ya zo ne a daidai lokacin da shugaban ƙasa ya tura wa majalisar sunayen mataimakan gwamnan bankin guda biyu domin tantancewa.

Ya ƙara da cewa za su yi amfani da damar wajen yi wa shugabannin tambayoyi kan sabon tsarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: