Hukumar asusun adashen lafiya na jihar Jigawa ta ce nan ba da jimawa ba daliban manyan makarantu za su cin gajiyar shirinta

0 73

Hukumar asusun adashen lafiya na jihar Jigawa ta ce nan ba da jimawa ba daliban manyan makarantu za su cin gajiyar shirinta.

Sakataren zartarwa na hukumar Dr Nura Ibrahim ya bayyana haka a cikin wani shirin rediyon Jigawa.

Ya ce tuni Kwalejin Ilimi ta Gumel ta gabatar da jerin sunayen dalibai dubu biyar da suka yi rajista wadanda za su ci gajiyar shirin.

Dokta Nura Ibrahim ya bayyana fatan nan da wata mai zuwa hukumar za ta kammala yi wa daukacin daliban manyan makarantu rajistar shirin.

Ya ce hukumar za ta yi amfani da cibiyoyin kiwon lafiya na makarantu.

Nura Ibrahim ya kara da cewa za a karbi naira dubu biyu daga hannun dukkan daliban manyan makarantun a matsayin gudunmawar kowace shekara.

A cewarsa, nan ba da jimawa ba ma’aikatan hukumar za su ziyarci dukkanin cibiyoyin lafiya da ke cikin shirin domin dubawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: