Rashin walwalar ma’aikatan gwamnati ke kara rura wutar cin hanci da rashawa a bangaren aikin gwamnati – Goodluck Jonathan

0 93

Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yace rashin tabbas akan walwalar ma’aikatan gwamnati ke kara rura wutar cin hanci da rashawa a bangaren aikin gwamnati.

Ya fadi haka jiya yayin kaddamar da wani littafi da tsohon limamin cocin fadar shugaban kasa, Obioma Onwuzurumba ta rubuta.

Bikin kaddamar da littafin, wanda kuma aka hada da kaddamar da cibiyar kula da dattawa, yazo ne a ranar bikin cikar wanda ya rubuta littafin, shekaru 73 a duniya.

Tsohon shugaban kasar ya koka bisa yadda ake watsi da rayuwar ma’aikatan gwamnati, wadanda yace an haramta musu shiga harkokin kasuwanci sannan kuma ba a kula da su idan sun yi ritaya daga aiki.

Ya yabawa wanda ya rubuta littafin tare da matarsa bisa kaddamar da cibiyar kula da dattawa.

Kazalika, shugaban bikin kuma tsohon ministan labarai, Farfesa Jerry Gana, ya koka bisa yadda gaskiya da amana suka yi karanci tsakanin ‘yan Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: