Shugaba Joe Biden ya yabawa shugaban kasa Buhari bisa kokarinsa na karfafa mulkin demokradiyya a kasashen Afrika

0 67

Shugaban Amurka Joe Biden ya yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa kokarinsa na karfafa mulkin demokradiyya ba a Najeriya kadai ba, har ma a sauran kasashen Afrika.

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, yace shugaban Amurkan ya fadi haka a birnin Washington na Amurka, yayin da yake ganawa da shugabannin kasashen Afrika 6, wadanda za su gudanar da zabuka a shekarar 2023.

An gudanar da zaman ganawar a gefen taron gwamnatin Amurka da shugabannin kasashen Afrika wanda ake yi a babban birnin Amurka.

Shugaba Biden yace yana bibiyar ayyukan shugaba Buhari tun shekarar 2015 lokacin da aka zabe shi shugaban kasa daga jagoran ‘yan adawa, a lokacin da shi Joe Biden yake mataimakin shugaban kasar Amurka.

Ya kara da cewa abin farinciki ne kasancewar Najeriya ta zama abar koyi a demokradiyya, musamman yadda Shugaban Buhari baya neman wa’adi na uku.

A saboda haka, Joe Biden, ya karfafa gwiwar shugaba Buhari da hukumar zaben Najeriya su cigaba da kasancewa matsayin ‘yan ba ruwanmu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: