Ku gaggauta yanke min hukuncin kisa domin bana tsoron mutuwa – Malam Abduljabbar

0 92

Malamin addinin Kano da ke fama da rikici, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara, ya bukaci babbar kotun shari’ar musulunci dake zama a kofar kudu dake jihar Kano da su gaggauta yanke masa hukuncin kisa, inda yace baya tsoron mutuwa.

Kotun karkashin jagorancin Ibrahim Sarki Yola a jiya ta yankewa Abduljabbar Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya.

An gurfanar da Abduljabbar Kabara bisa zargin kalaman batanci ga Annabi Muhammad SAW a wasu daga cikin karatuttukansa.

Da yake magana a kotun jim kadan bayan an yanke masa hukuncin, Abduljabbar Kabara yayi kiran da a gaggauta zartar masa da hukunci, inda yace baya tsoron mutuwar shahada.

Sai dai, malamin ya zargi alkalin da sauya dukkan hujjojin da aka gabatar.

Da yake zartar da hukunci, Ibrahim Sarki Yola, yace ya amince da dukkan hujjojin da masu kara suka gabatar, inda yace sun tabbatar da dukkan tuhume-tuhumen da suke masa ba tare da wani shakku ba.

Bayan hakuncin kisan ta hanyar rataya, mai shari’ar ya kuma bada umarnin gaggawa na kwace dukkanin littafan malamin da kuma masallatansa 2, wanda da su ne yayi amfani wajen aikata laifin da ake tuhumar sa da aikatawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: