Gwamnatin Tarayya ta Zargi Peter Obi da Jefa Kasar cikin Rikici.

0 148

Gwamnatin tarayya ta zargi dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar Labor, Peter Obi da cin amanar kasa tare da kuma tunzura jama’a domin jefa kasar cikin rikici bayan ya fadi a zaben 2023.

Ministan labarai da al’adu Alh Lai Muhammad ne ya bada wanna gargadi da birnin Washington gundumar kwalanbiya ta Amurka yayi da yake zantawa da kafafan yada labarai na duniya.

Kamfanin dillancin labarai na kas NAN ya bada rahotan cewa mininstan yace Washington ne domin yayi karin haske dangane da sakamakon zaben na wannan shekarar.

Lai Muhammad yace kuskure ne Peter Obi yayi yunkurin zuwa kotu domin kalubalantar sakamakon zaben domin haka zai tunzura matasa.

A cewar ministan, ko Peter yaje kotu ko bai je ba dokar kasa tana da hurumar bayyana wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: