Gwamnatin Tarayya zata ciyo bashin dala miliyan 500 daga Bankin Duniya

0 109

Gwamnatin Tarayya na neman rancen dala miliyan 500 daga Bankin Duniya domin bunkasa ababen more rayuwa da hanyoyin karkara da bunkusa  kasuwancin noma a fadin kasar nan.

Gwamnat tace ana sa ran bashin zai magance bukatun da ake dasu a yankunan karkara dake kasar nan, inda tace a halin yanzu mutane miliyan 92 ba su da hanyoyi masu kyau.

Wannan bukatar na kunshe ne a cikin daftarin karshe na Tsarin Manufofin sake Matsugunni na Ma’aikatar Aikin Gona da Raya Karkara ta Tarayya da tsarin samar da hanyoyin Karkara da bunkasa noma a Najeriya. Aikin na da nufin inganta hanyoyin shiga yankunan karkara ta yadda za a kara bunkasa noma da kuma bunkasa kasuwacin manoman karkaran

Leave a Reply

%d bloggers like this: