Gwamnatin Tarayya zata gina gidaje 100 a kowacce karamar hukuma a fadin kasar nan, kamar yadda Ministan Gidaje na Ƙasa, Yusuf Atta, ya bayyana a Kano yayin da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, ke karɓar daruruwan masu sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC.
Ministan ya bayyana cewa jimillar gidaje dubu 77,400 za a gina a fadin ƙasar, inda jihar Kano zata samu guda 4,400, bisa shirin “Renewed Hope Housing Agenda” na Shugaba Bola Tinubu.
Atta ya bayyana wannan mataki a matsayin babbar dama da zata inganta rayuwar al’umma da kuma samar da mafita ga matsalar rashin masauki, musamman ga marasa galihu.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Kano da su goyi bayan gwamnatin Tinubu domin ci gaba da samun cigaba mai ma’ana.