Shugaban kasa Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyaran gadar Mokwa da ambaliya ya lalata a jihar Neja

0 123

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin gaggauta gyaran gadar Mokwa da ke jihar Neja wadda ambaliya ta lalata kwanan nan.

Rushewar gadar ta yanke muhimmin hanyar da ke haɗa arewa da kudancin ƙasar, abin da ya tayar da hankula a fadin ƙasa.

Ministan Ƙananan Ayyuka, Bello Goronyo, ya bayyana hakan a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummar Mokwa a madadin shugaban ƙasa. A cikin jawabinsa, Goronyo ya ce shugaban ƙasa ya nuna damuwa matuƙa game da halin da jama’a ke ciki, tare da bayyana cewa wajibi ne a gyara gadar da kuma buɗe hanyoyin da manyan motocin haya za su rika wucewa ba tare da cikas ba.

Leave a Reply