Tunji Alausa ya gargadi jami’o’i da kwalejojin fasaha kan kafa sabbin cibiyoyin karatu ba bisa ka’ida ba
Ministan Ilimi na Tarayya, Dr. Tunji Alausa, ya fitar da sabon gargaɗi ga jami’o’i, kwalejojin fasaha da na ilimi na tarayya, inda ya ce dole ne su daina kafa sabbin cibiyoyin karatu ba tare da izini daga hukumomin da suka dace ba.
A cikin wata wasiƙa zuwa ga shugabannin NUC, NBTE da NCCE, ministan ya nuna damuwa kan yawaitar kafa cibiyoyi ba tare da ingantattun kayayyakin aiki, tsarin karatu da goyon bayan ababen more rayuwa ba.
Ya ce wannan abu yana rage darajar ilimi a Najeriya, kuma yana rage inganci da dorewar tsarin ilimi. Ya gargadi shugabannin cibiyoyin da cewa duk wanda ya karya wannan doka zai fuskanci hukunci mai tsanani daga gwamnatin tarayya.