Gwamnatin tarayyana Shirin hada hannu da kamfanonin samar da ababen hawa masu amfani da lantarki a wani bangare na komawa tsarin amfani da motoci masu lantarki maimakon masu amfani da fetur.
Drakta janar na hukumar tsara kayan sufurin masu lantarki Jelani Aliyu, shine ya bayyanahakan, tare da cewa ana saran zai samu sahalewa a dokance kafin karshen shekarar da muke ciki.
Jilani Aliyu yayi wannan jawabin ne a jiya yayin wani horo da kungiyar yan jarida ta shirya a birnin legas.
Jilani wanda ya halarci taron ta bidiyon kai tsaye ya jajjada cewa kasashen duniya da dama sun shiga yunkurin samar da ababen hawan masu amfani da lantarki, irin turbar da Najeriya ta sanya a gaba.
A kwanakin baya ne dai gomnatin tarayya ta kaddamar da motar farko da aka kirkira a Najeriya mai amfani da lantarki, ta kamfanin Hyundai Kona, abinda yasa hakuma NDDC ta kaddamar da guraren chajin motocin guda biyu a birnin Sokoto da kuma legas.