Gwamnonin kudancin kasarnan sun ce dole ne shugaban kasa ya fito daga yankin su a zaben 2023

0 120

Gwamnonin kudancin kasarnan sun ce dole ne shugaban kasa ya fito daga kudancin kasar a zaben shekara ta 2023.

A wani taro da suka gudanar a jihar Enugu, gwamnonin sun jaddada wasu yarjejeniyoyi da suka cimma wanda Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, shugaban kungiyar gwamnonin ya fada a wata sanarwa.

Yarjeniyoyin sun hada da bukatar gwamnonin yankin ta dan yankin ya zama shugaban kasa a 2023 da jaddada bukatarsu ta shigar da gyaran da suke so a yi a kundin tsarin mulki da batun hana kiwo da kuma batun harajin kayayyaki na VAT.

Kan batun hana kiwo, kungiyar gwamnonin ta ce ta gamsu da yadda jihohin kudu ke kawo gyara cikin dokokin kiwo a fili kuma Gwamna Akeredolu ya ce sun bukaci sauran jihohin yankin da ba su sa dokokin hana kiwon ba, da su yi hakan.

Haka kuma, ya ce jihohin yankin na da yancin kafa harajin VAT da ake samu daga jihohin, lamarin da ya janyo jayayya tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: