Wani hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutum biyar yayin da wasu takwas suka ji raunuka a ƙaramar hukumar Billiri ta jihar Gombe.
Lamarin ya faru ne a lokacin da birkin wata mota ɗauke da kayan abinci ya shanye, inda ta kutsa cikin dandazon jama’a da ke gudanar da bukukuwan Easter na mabiya addinin Kirista.
Wata da ke halartar bukukuwan ta shaida wa manema labarai cewa ɓacin rai ne ya sa mutane suka ƙona motar nan take.
Rundunar ‘yansanda a jihar ta ce cikin waɗanda suka jikkata har da wasu Musulmai da ke sallah a gefen titi.
Ismaila Uba Misilli, shi ne babban jami’in yaɗa labarai na gwannan jihar ta Gombe. Ya ce zuwa yanzu hankula sun kwanta a yankin kuma ana ci gaba da harkoki kamar yadda aka saba.
Gwamnatin jihar Gombe ta ɗauki nauyin kudin magunguna na ɗaukacin waɗanda suka ji raunuka sakamakon ibtila’in.