- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Hukumar Alhazai ta Kasa ta bukaci hukumomin jin dadin alhazai na jihoshi da su sake sabunta ayyukansu na aikin Hajjin bana.
Shugaban hukumar Zikrullah Hassan ne ya bada wannan umarni a jiya yayin wata ganawa da manyan jami’an kungiyoyin na jihoshi a helkwatar hukumar dake Abuja.
Zikrullah Hassan ya bayyana cewa makasudin taron shi ne a samu kulla alakar huldar da aka saba tsakanin hukumar da manyan jami’an hajji na jihoshi.
Zikrullah Hassan ya ce tuni aka kulla yarjejeniya tsakanin Najeriya da Saudiyya dangane da aikin Hajjin bana.
A saboda haka ya jaddada bukatar dukkan manyan jami’an hukumar su kasance cikin shirin cewa aikin Hajji bana zai iya gudana.
Shugaban ya bayyana cewa shirin adashen gata na aikin hajji zai taka muhimmiyar rawa sosai wajen daukar maniyyatan aikin hajjin bana.