Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Jigawa ta bukaci daliban jihar da su shiga shafin ta na yanar gizo domin cike form na samun tallafin karatu

0 201

Hukumar bada tallafin karatu ta jihar Jigawa, scholarship board ta bukaci daliban jihar nan da suka sami guraben karatu a manyan makarantun kasar nan da su tabbatar sun shiga shafin sadarwa na hukumar domin cike form na samun tallafin karatu

Sakataren zartarwa na hukumar, Mallam Saidu Magaji, ya sanar da hakan a lokacin ganawa da wakilinmu

Ya ce hakan na daga cikin kudirin gwamna Mallam Umar Namadi na ganin daliban Jigawa sun sami kudin tallafi domin samun damar yin rijista a makarantun da suka sami guraben karatu

Mallam Saidu Magaji ya kara da cewar a ranar litinin mai zuwa ne hukumar zata fara ziyartar manyan makarantu domin ganawa da daliban da suka cike form din hukumar ta kafar sadarwa ta zamani domin samun tallafin karatunsu akan lokaci

Ya shawarci daliban da su shiga shafin sadarwa na hukumar jssb.ng domin cikewa akan lokaci

Mallam Saidu Magaji ya ce da zarar an tantance dalibi ko daliba zasu sami tallafin karatun su ba tare da bata lokaci  ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: