Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu jami’an banki kan zargin damfarar kudi kimanin naira biliyan 8.568

0 264

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta gurfanar da wasu jami’an banki guda uku tare da wasu mutane hudu a gaban kotun tarayya da ke Legas kan zargin hada baki da damfara da ya kai kimanin naira biliyan takwas da miliyan dari biyar da sittin da takwas.

Wadanda ake tuhuma su ne Samuel Ihechukwu Asiegbu, da Fabian Onyeimachi da Kingsley Ejim Kelechi daga bangaren ma’aikatan banki, tare da Hannah Okunlola Adesokan, da Hamza Zakariya, da Achionu Ubaku da Sunday Osademe, wadanda ake zargi da canza bayanai a cikin tsarin kwamfutar banki domin su karɓi kudi ta hanyar yaudara a watan Janairu na shekarar nan.

EFCC ta ce laifin ya sabawa sashe na 27 sakin layi na ɗaya (a) na dokar hana laifukan yanar gizo ta shekarar 2015, kuma bayan karanta musu tuhume-tuhume guda takwas da ake yi musu, dukkansu sun musanta zargin. Mai shari’a Daniel Osiagor ya umarci a tura su gidan gyaran hali na ƙasa, sai dai Hannah Okunlola za ta ci gaba da zama a hannun EFCC saboda yanayin lafiyarta, yayin da aka tabbatar da belin Kingsley Ejim Kelechi da aka ba shi a baya, sannan aka dage cigaban shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Yuni mai zuwa.

Leave a Reply