Hukumar hana fataucin mutane ta kasa ta ceto tare da karbar mutane 21,181 da aka yi fataucin su

0 263

Hukumar hana fataucin mutane ta kasa ta ceto tare da karbar mutane dubu 21 da 181 da aka yi fataucin su cikin shekaru 20.

Darakta Janar na Hukumar ta NAPTIP, Farfesa Fatima Waziri-Azi, ta bayyana hakan a lokacin data bayyana a gaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin jin dadin jama’a yayin kare kasafin kudin 2024.

Ta ce hukumar za ta yi kokarin tallafa wa wadanda abin ya shafa matukar suna bukatar a tallafa musu, inda ta ce tsarin na bukatar lokaci da kuma kudade.

Ta bayyana cewa hukumar ta NAPTIP tana bada tallafi domin gyara rayuwar wadanda abin ya shafa.

Waziri-Azi ta bayyana cewa, a shekarar 2022, hukumar ta NAPTIP ta ceto tare da karbar mutane dubu 2 da 748 wadanda aka yi safarar su. Ta kara da cewa, “Daga watan Janairu zuwa Nuwamba 2023, hukumar ta ceto tare da karbar mutane dubu 2 da 200 da aka yi safararsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: