Kasafin kudin shekarar 2024 ba zai fuskanci maimaicin ayyuka ba – Philip Agbese

0 186

Mataimakin kakakin majalisar wakilai,ta kasa Philip Agbese, ya ce kasafin kudin shekarar 2024 ba zai fuskanci maimaicin ayyuka ba.

Da yake magana a cikin shirin Sunrise Daily na gidan Talabijin na Channels a jiya, ya ce kididdigar kasafin kudin shekarar 2023 za ta fi yin nazari fiye da yadda aka saba yi a Majalisar kasar da ta gabata.

A shekarar 2022, hukumar yaki da cin hanci da rashawa da sauran manyan laifuka ta (ICPC) ta bayyana cewa ma’aikatu, da hukumomi sun zaftare kasafin kudin 2021 da kusan naira bilyan 300 ta hanyar kwafin wasu ayyuka da aka yi a baya. A ranar 29 ga Nuwamba, 2023, Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kudin sa na farko na kimanin sama da naira tiriliyab 27 na shekara ta 2024 ga Majalisar kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: