Gwamnatin tarayya ta sanar da fara aiwatar da dokar kare hakkin masu lalurar nakasa

0 195

A wani yunkuri na kare hakkin nakasassu da inganta rayuwarsu a Najeriya, gwamnatin tarayya ta sanar da fara aiwatar da dokar kare hakkin masu lalurar nakasa daga watan Janairu.

Sawaba ta ruwaito cewa Majalisar kasa ta zartar da dokar kare hakkin nakasa a watan Janairun 2019, bayan shekaru da dama da masu fafutukar kare hakkin nakasa sun yi kira da aiwatar da dokar.

Sai dai har yanzu ba a fara aiwatar da dokar ba.

Dokar ta shafi haƙƙoƙi da dama, wadanda suka hada da  haramcin nuna wariya ga nakasassu a fannoni daban-daban, kamar ilimi, da samar da aikin yi, da kiwon lafiya, da sauransu.

Sakataren zartarwa na hukumar nakasassu James David Lalu shine ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar jiya a Abuja.

Ya ce matakin na da nufin kawar da nuna wariya tare da tabbatar da daidaito ga kowane dan kasa ba tare da la’akari da karfin jiki ko tunani ba.

David ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na kara inganta hada kan al’umma da, samun daidaito, da adalci ga nakasassu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: