Hukumar Hisbah ta fara kama wanzamai da matasan da ke askin zamani

0 583

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce ma’aikatan hukumar Hisbah na ƙungiyar Taliban a Afghanistan na tsare wanzamai da matasan da ke askin da ta ce ya saɓa wa ƙa’ida da kuma tsawaita gemu.

Kamen na zuwa ne bayan da a watan Agustan bara ma’aikatar ɗa’a da yaƙi da miyagun ɗabi’a ta aiwatar da dokokin da za su riƙa lura da yanayin askin matasa tare da haramta wa mata magana a bainar jama’a.

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya ce dokokin na haifar da mummunar makoma ga ƙasar.

Sai dai tuni ƙungiyar Taliban ta yi watsi da sukar.

Leave a Reply