Hukumar ICPC tana shirin fara binciken ayyukan gwamnatoci da na ‘yan majalisa

0 62

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifukan (ICPC) ta ce tana shirin fara kashi na uku na binciken ayyukan gwamnatoci da na ‘yan majalisa.

Mai magana da yawun ICPC, Azuka Ogugwa, a cikin wata sanarwa a jiya ya ce za a gudanar da aikin bin diddigin a jihohi 17 da babban birnin tarayya.

Baya ga Babban Birnin Tarayya, jihohin sune: Katsina, Kano, Sokoto, Yobe, Adamawa, Plateau da Kogi. Sauran sune Benue, Ondo, Osun, Lagos, Bayelsa, Akwa Ibom, Enugu, Edo, Anambra da Imo.

Hukumar ta ce aikin bin diddigin zai mayar da hankali kan muhimman fannoni da suka hada da noma, ilimi, wutar lantarki, kiwon lafiya da albarkatun ruwa.

Ta ce za a binciki ayyukan ‘yan majalisa dubu 1 da 24 da ayyukan gwamnatoci 227, jumillar ayyukan dubu 1 da 251, wadanda aka warewa kudade a kasafin kudin shekarar 2019 da 2020.

Leave a Reply

%d bloggers like this: