Shugaba Buhari ya sauke ministocin ma’aikatun Noma dana Lantarki, Sabo Nanono da kuma Sale Mamman

0 72

Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke ministoci biyu na ma’aikatun Noma Sabo Nanono da kuma na Lantarki Sale Mamman.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Najeriya, Femi Adesina ya fitar a wannan Larabar.

Sanarwar ta ce Ministan Muhalli, Mohammed Abubakar ne zai maye gurbin Ministan Noma, yayinda karamin Ministan ayyuka, Abubakar Aliyu zai maye gurbin Ministan Lantarki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: