Hukumar Immigration reshen jihar Jigawa ta ceto mutane shida da aka yi safararsu

0 125

Hukumar shige da fice ta kasa, Immigration, reshen jihar Jigawa, ta ce ta ceto mutane shida da aka yi safararsu a jihar.

Kwanturolan hukumar a jihar, Ahmed Bagari, ya shaida wa manema labarai jiya a birnin Dutse cewa, jami’an hukumar ne suka ceto wadanda abin ya shafa a ranar Lahadi.

Ahmed Bagari wanda mataimakin kwanturola na hukumar shige da fice Muhammad Yako ya wakilta ya ce, an ceto mutanen da misalin karfe 6 da rabi na yamma, a wani gini da ba a kammala ba a garin Babura, hedikwatar karamar hukumar Babura ta jihar.

Ya bayyana cewa, wadanda abin ya shafa, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 35, an ceto su ne a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa kasar Libya bayan sun ratsa ta Jamhuriyar Nijar.

Kwanturolan ya kara da cewa wadanda aka ceto, mata ne biyar da kuma namiji daya wadanda suka fito daga jihohin Oyo da Nassarawa.

A cewarsa, babu daya daga cikin wadanda aka ceto da ya mallaki wata takardar tafiya sannan kuma ba a same su dauke da wani abun laifi ba, yayin da ake yi musu tambayoyi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: