Kashi mafi yawa na ƙasashen duniya za su shiga cikin babban matsin tattalin arziki – IMF

0 199

Shugabar asusun bayar da lamuni na duniya IMF, Kristalina Georgieva, ta ce tattalin arzikin duniya na cikin mummunan yanayi, inda ta yi gargaɗin cewa kashi ɗaya bisa uku na ƙasashen duniya za su fada cikin matsalar tattalin arziki.

Kasashen duniya ta dama sun shiga matsin tattalin arziki a shekarar 2022, sakamakon yaƙin Ukraine da annobar cutar korona da kuma hauhawar farashin kayyaki wanda ya shafi ƙasashen duniya da dama ciki har da manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki.

Misis Georgieva, ta ce manyan ƙasashe masu ƙarfin tattalin arzikin ka iya fuskantar barazanar faɗawa cikin matsin tattalin arziki a wannan sabuwar shekara da aka shiga.

”Mun yi hasashen cewa kashi ɗaya bisa uku na ƙasashen duniya za su faɗa cikin matsin tattalin arziki a wannan shekara” kamar yadda ta bayyana wa kafar yaɗa labarai ta CBS.

Leave a Reply

%d bloggers like this: