Shugaban kamfanin BUA ya baiwa jami’ar Alqalam tallafin kudi na naira miliyan 250 domin bunkasa ababen more rayuwa

0 118

Jami’ar Al-Qalam ta Katsina ta yabawa shugaban rukunin kamfanin BUA, Abdulsamad Rabi’u da ya baiwa jami’ar tallafin kudi na naira miliyan 250 domin bunkasa ababen more rayuwa.

Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Nasiru Yauri, ya yi wannan yabon ne a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma ya rabawa manema labarai jiya a Sakkwato.

A cewar Nasiru Yauri, tallafin da aka bayar ta karkashin shirin Abdulsamad Rabiu Africa Initiative yana da matukar tasiri wajen magance matsalar karancin ababen more rayuwa a manyan makarantu.

Mataimakin shugaban jami’ar ya bayyana fatansa na cewa tallafin na Abdulsamad Rabiu Africa Initiative zai taimaka wajen bunkasa kwazon manyan makarantun da kuma ba su damar bayar da gudunmawa mai ma’ana ga ci gaban kasa.

Ya yi kira ga wadanda suka ci gajiyar tallafin da su nuna sakkayya ga karamcin attajirin ta hanyar amfani da tallafin ta hanyar da ta da ce.

Leave a Reply

%d bloggers like this: