Garba Shehu bayyana Obasanjo a matsayin mutum marar da’a da ke sukar shugabanni saboda son kansa

0 116

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Mallam Garba Shehu, ya bayyana tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a matsayin mutum marar da’a da ke sukar shugabanni saboda damuwar dake ransa.

A cikin wata wasika, Olusegun Obasanjo ya yi ikirarin cewa Muhammadu Buhari ya durkusar da kasar nan kasa da matsayin da ta ke akai a shekarar 1999.

Da yake mayar da martani, Garba Shehu a wata sanarwa da ya fitar a jiya, ya ce Olusegun Obasanjo sananne ne ga kowa, wanda babu wanda ke bukatar a bayyana masa ko wanene shi.

A wani batun kuma, daraktan yada labarai na majalisar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bayo Onanuga, ya ce amincewa da Peter Obi, da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi, ba shi da amfani.

Bayo Onanuga a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ya ce Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023 ba zai taba damuwa ba kan Obasanjo saboda ya yi kaurin suna wajen adawa da ’yan siyasa masu neman kawo ci gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: