Hukumar JAMB ta sanar da cire wasu cibiyoyi guda biyar daga jerin wuraren gudanar da jarabawar UTME ta 2025 saboda gaza bin ƙa’idoji da kuma gazawar na’urori, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Cibiyoyin da abin ya shafa sun haɗa da wasu a Kano, Sokoto da Imo, inda aka buƙaci ɗalibai da su sake buga takardun neman zana jarabawa domin sanin sabon wurin da aka tura su.
JAMB ta kuma bayyana cewa sama da ɗalibai 900,000 sun kammala jarabawar cikin nasara daga cikin sama da miliyan biyu da suka yi rajista.
Haka kuma, hukumar ta yi gargadi da cewa duk wata cibiya da ta kasa bin ƙa’idoji, za a hukunta ta ba tare da la’akari da mallakinta ba, sannan ta bayyana kama mutane 27 da ake zargi da damfara.