Gwamnatin Jigawa ta bukaci jama’a da su kai rahoto kan duk dillalin da ke kokarin bata shirin Noma

0 466

Gwamnatin jihar Jigawa ta bukaci jama’a da su rika kai rahoto kan duk wani dillalin kayan gona ko mutum da ke kokarin bata shirin noman shinkafar damina na bana a jihar.

Da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa, mai ba gwamna shawara na musamman, Dokta Saifullahi Umar, ya bayyana cewa wannan shiri wani bangare ne na cigaban noman shinkafa a Jigawa, domin kara habbaka samar da shinkafar.

Ya kara da cewa, jihar Jigawa ce ta biyu mafi yawan samar da shinkafa a Najeriya da ton miliyan biyu a kowace shekara, inda a bana za a bai wa manoma 58,000 kayan tallafi bisa wani tsari da suka kira “Catalyst Package”.

Dokta Saifullahi ya ce an tanadi nau’o’in tallafi dabam-dabam ga kananan manoma da manyan manoma, inda akalla kashi 80 cikin 100 na wadanda za su amfana za su samu ragin kudin kayan aiki daga kashi 20 zuwa 30 cikin 100, tare da tsauraran matakan dakile duk wani kokarin damfara, yana mai bukatar jama’a su rika ba gwamnati rahoton duk wani abu da suka lura da shi.

Leave a Reply