‘Yan kasuwar da suka ajiye amfanin gona musamman dangin hatsi a jihohin Neja sun damuwarsu sakamakon faduwar farashin kayan abinci da ke ci gaba da faruwa tun watan Oktoba na bara.
Rahotanni na nuni da cewa wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun nemi rancen makudan kudade daga bankunan kasuwanci, wasu kuma sun sayar da kadarorinsu, suna fata farashin kayan abinci zai tashi kamar yadda ya yi a shekarar 2024.
Yanzu haka kuwa, farashin buhun wake da aka sayar da shi a sama da N200,000 a bara, ya fadi zuwa N96,000.
A wasu kasuwannin karkara irin su Zungeru, Beji da Manigi, rahotanni na cewa masu ajiye hatsi suna ci gaba da fuskantar asarar dukiyarsu yayin da kasuwar ke kara durkushewa, inda wasu ke kokarin sayar da kayayyakinsu da gaggawa don kauce wa karin hasara.