Akalla mutane 28 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara

0 97

Rahotanni na nuna cewa akalla mutane 28, ciki har da ma’aikatan hakar ma’adanai 20, suka rasa rayukansu a hare-haren da ‘yan bindiga suka kai cikin kewayen karamar hukumar Maru a ranar Alhamis da karfe 11:30 na safe.

Maharan sun kai farmaki kauyukan Gobirawa Chali, Damaga da Lugga, inda aka bayyana hare-haren a matsayin na bazata da kuma cin fuska, inda aka ce ‘yan bindigar sun zo da dimbin yawan su.

A Gobirawa Chali ne aka fi samun hasarar rayuka, inda aka kashe sama da ma’aikata 20 a wurin hakar ma’adanai, kamar yadda wani mazaunin kauyen, Ismail Hassan, ya shaida wa Reuters cewa, ‘yan bindigan da yawansu suka budewa ma’aikata wuta. Hukumar Amnesty International ta tabbatar da cewa an kai farmakin ne har da shiga gida-gida ana kashe mutane, lamarin da ya sake tona matsalar rashin tsaro da ke addabar Zamfara, duk kuwa da kokarin da rundunar soji ke yi a yankin.

Leave a Reply