Watan Zul’kida bai kama ba a Najeriya – Fadar Sarkin Musulmi

0 505

Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya Muhammad Sa’ad Abubakar III ta ce ranar Talata ce 1 ga watan Zulki’ida na shekarar Hijira ta 1446.

Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga jaririn watan ba a ranar Lahadi.

A ƙa’idar kalandar Musulunci, kowane wata yana yin kwana 29 ne, amma idan ba a ga jaririn watan ba sai a cika shi zuwa kwana 30.

Hakan na nufin yau Litinin 28 ga watan Afrilu ne 30 ga watan Ƙaramar Sallah na Shawwal.

Leave a Reply