‘Yan siyasa na rikici da juna ne don samun mukamai ba dan jin dadin jama’a ba – Attahiru Bafarawa

0 554

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto, Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, yayi gargadin cewa adawa na cikin tsakan mai yuwa a halin yanzu yayin da yake cewa babu wata sahihiyar jam’iyyar adawa a siyasar Najeriya.

Bafarawa, wanda ya kasance jigo a jam’iyyar PDP, ya fice daga jam’iyyar a ranar 13 ga Janairu, 2025, bayan rubuta wasika zuwa ga shugabannin jam’iyyar inda ya ce yana son mayar da hankali kan shirye-shiryen tallafa wa matasa.

Yayin wata hira da ya yi da BBC Hausa da wakilin su ya saurara, tsohon gwamnan ya bayyana cewa ‘yan siyasa a Najeriya sai dai su rika fafatawa domin samun mukamai, ba wai suna yi wa talakawa aiki ba.

Ya yi wannan bayani ne biyo bayan sauya shekar da wasu fitattun ‘yan adawa ke yi zuwa jam’iyyar APC mai mulki, a shirye-shiryen zaben 2027.

Bafarawa ya ce sauya shekar da ake yi na da manufa ta son kai, ba don amfanin jama’a ba, yana mai jaddada cewa “siyasar adawa ta mutu a kasar nan.”
Ya koka kan yadda ‘yan siyasa ke rikici da juna kawai don samun mukamai, ba tare da la’akari da jin dadin jama’a ba.

Leave a Reply