Hukumar samar da guraben karatu a makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta dage ranar fara rijistar jarabawar UTME da DE.

A baya an tsara fara rijistar daga ranar 12 zuwa 19 ga watan Maris na bana, sai dai hukumar ta dage ranakun inda za a fara ranar 19 a kare a ranar 26 ga watan Maris na bana.

Shugaban sashen hulda da jama’a na hukumar, Fabian Benjamin, cikin wata sanarwa da ya fitar a yau yace anyi karin mako daya domin kammala dukkan shirye-shiryen da suka kamata domin aikin rijistar.

Yace aikin wanda za a kammala cikin sati 1, ana kuma sa ran samun bayanai daga masu rubuta jarabawar da kuma masu ruwa da tsaki.

Da yake nuni da cewa hukumar a shirye take ta samar da aiki mai inganci ga ‘yan Najeriya, yace za a sanar da sabbin ka’idojin rijistar UTME a ranar Litinin mai zuwa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: