Hukumar Kare Haƙƙin Bil Adama Ta MƊD Ta Kaɗa Ƙuri’ar Ƙara Sa Ido Kan Matsalolin Cin Zarafin Bil Adama A Kasar Sudan

0 86

Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta kaɗa ƙuri’ar ƙara sa ido kan matsalolin cin zarafin bil adama a kasar Sudan.

Ƙasashe 18 ne suka kaɗa ƙuri’ar amincewa da tsarin ƙarƙashin jagorancin ƙasashen yamma a wani taro na musamman a Geneva yayin da wasu 15 kuma suka nuna adawa sai 14 da suka ƙaurace.

Sudan da kanta ta yi fatali da kudirin inda ta ce rikicin batu ne na cikin gida.

Tun farko dai, taron ya saurari kiraye-kirayen a gaggauta tsagaita wuta domin taimaka wa ƙoƙarin da ake na shigar da kayayyakin agajin da ake buƙata zuwa Sudan. An kashe ɗaruruwan fararen hula tun bayan da yaƙin ya ɓarke a watan da ya gabata tsakanin ɓangarorin da ke rikici da juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: