Wasu Fusatattun Zababbun Yan Majalissu Sun Nuna Rashin Amincewa Da Zabin Da Jam’iyyar APC Tayi

0 91

A cigaba da shirye-shiryen kaddamar da sabuwar majalissa ta 10 a watan Yuni mai zuwa, wasu daga cikin fusatattun zababbun yan majalissu na jam’iyyar APC sun je hedikwatar jam’iyyar ta kasa dake babban birnin tarayya Abuja domin nuna rashin amincewar su bisa zabin da uwar jam’iyyar ta yi.

Zababbun sanatocin da suka kalubalanci matakin sun hada da Senators Abdulaziz Yari, Orji Kalu, Mohammed Musa, da kuma Sadiq Umar.

Sun kuma samu damar ganawa da shugaban  jam’iyyar APC Abdullahi Adamu da  Secretary Iyiola Omisore da kuma shugabar jam’iyyar ta mata Beta Edu.

Idan zamu iya tunawa dai a ranar litinin ne jam’iyyar APC ta raba mukaman majalissar.

Wadanda aka nada sun hada Senator Godswill Akpabio (Akwa Ibom) a matsayin shugaban majalissa sai mataimakin sa Senator Barau Jibrin (Kano). Sauran sun hada da kakakin majalissa Abbas Tajudeen (Kaduna) sai mataimakin kakakin majalissa Ben Kalu (Abia).

Leave a Reply

%d bloggers like this: