Jiragen Yakin Kasar Isra’ila Sun Kashe Wani Babban Kwamandan Kungiyar Jihadin Islama Ta Falasdinawa A Gaza

0 86

Wani hari da jiragen yakin kasar Isra’ila suka kai da sanyin safiyar yau ya kashe wani babban kwamandan kungiyar Jihadin Islama ta Falasdinawa da wasu ‘yan ta’adda biyu a Gaza.

Sojojin Isra’ila sun ce an kashe su ne a wani hari da aka kai a wani gida da ke bene hawa na biyar na wani gini a kudancin kasar.

A jiya ne kungiyar Jihadin Islama a Gaza ta harba rokoki sama da 500 zuwa kasar Isra’ila.

Sojojin Isra’ila sun kai hari kan gurare sama da 130 a Gaza, a fada mafi muni cikin watanni tara.

Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce mutane ashirin da biyar ne aka kashe a Gaza tun daga safiyar ranar Talata lokacin da Isra’ila ta fara kai farmaki kan ‘yan kungiyar Jihadin Islama, inda ta kara da cewa wadanda aka kashe sun hada da fararen hula akalla 10 da wasu kwamandojin kungiyar Jihadin Islama su uku.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce mutane 4 da suka hada da kananan yara 3 ne suka mutu a Gaza ta hanyar rokoki da suka ki harbuwa, sai dai majiyoyin Falasdinawa ba su tabbatar da hakan ba. Ba a samu asarar rai ba a Isra’ila, kodayake wasu rokoki sun afkawa gidaje da wasu gine-gine.

Leave a Reply

%d bloggers like this: