Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta ceto rayuka fiye da 1,000 da dukiyoyi kimanin miliyan 905 daga gobara 867 da aka samu a 2022

0 107

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano tace ta ceto rayuka dubu 1 da 35 da dukiyoyi da darajarsu ta kai naira miliyan 905 daga gobara 867 da aka samu a jihar daga watan Janairu zuwa Disambar 2022.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Saminu Yusuf Abdullahi, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.

Sai dai, Yusuf Abdullahi yace mutane 166 sun rasa rayukansu, yayinda aka yi asarar dukiyoyi na naira miliyan 358 a gobara daban-daban cikin shekarar.

Ya kuma ce hukumar ta kai dauki a hatsarin mota guda 575, yayin da ta ceto dabbobi 6 da suka makale.

Kakakin ya danganta gobara da aka samu a daban-daban da sakaci wajen amfani da gas na girki da kuma amfani da kayan wuta marasa inganci.

Ya shawarci jama’a da su kauracewa ajiye fetur a gida ko duk wani waje mara tsaro saboda karancin man fetur.

Yusuf Abdullahi ya kuma shawarci mazauna jihar da suke kiran hukumar idan suna bukatar daukin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: