Hukumar kula da alhazai ta kasa tace ta fara shirye-shiryen aikin hajjin badi, domin samun nasarar aikin.

Shugaban hukumar, Zirullah Hassan, shine ya sanar da haka a wajen bikin lakca da raba kyaututtuka na masu aiko da rahotannin aikin hajji masu zaman kansu da aka gudanar yau a dakin taro na babban masallachin kasa dake Abuja.

Shugaban hukumar, wanda ya samu wakilcin daraktan gudanarwa na hukumar, Ibrahim Sodangi, yace an fara shirye-shiryen a karshen aikin hajjin bana.

Tun ma kafin a kai alhazai kasar Saudiyya.

Yace hukumar ta gudanar da tattaunawar shirye-shirye tare da masu samar da masaukan alhazai da nufin samun masaukan da suka dace domin alhazan badi.

Shugaban yace hukumar tana shirin shirya taron kasa da kasa tare da kwararru daga sassa daban-daban na duniya, domin cigaba da tattaunawa akan hanyoyin samun nasarar aikin hajji.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: