Helkwatar tsaro tace dakarun operation Hadarin Daji sun kashe ‘yan ta’adda sama da 36 da wasu da dama a hare-haren jiragen saman da suka kai a yankin Arewa maso Gabas cikin makonni 2.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Musa Danmadami ya sanar da hakan a wajen taron manema labarai da ake gudanarwa sau biyu a sati akan ayyukan sojoji yau a Abuja.

Musa Danmadami yace manyan kwamandoji biyu na Boko Haram da ISWAP, masu suna Abu Asiya da Abu Ubaida, na daga cikin wadanda aka kashe cikin makonnin.

Yace bayan an kashe Abu Asiya a yankin Parisu, an kuma kashe Abu Ubaida a yankin Sheruri dukkansu a dajin Sambisa a ranakun 12 da 15 ga watan Satumba.

Kakakin na tsaro yace sojojin sama a ranar 9 ga watan Satumba sun kashe mayaka da dama a yankin Somalia na dajin Sambia a wasu hare-haren jiragen sama.

Yace an aiwatar da makamancin harin a maboyar mayaka dake Abdallari, da Mafa, da Zanari da kuma Tumbun Baba, tsakanin ranakun 10 zuwa 14 ga watan Satumba.

Inda aka kashe mayaka da dama tare da lalata gine-ginensu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: